Nigerian news All categories All tags
Kotu ta daure shi na watanni 5 don ya ma makwabcin sa sata

Kotu ta daure shi na watanni 5 don ya ma makwabcin sa sata

- Kotu ta aike da wani mutum gidan yari bayan an kama shi da laifin satan kayan makwabcinsa

- Wanda ake tuhuma ya amsa laifin sa kuma ya nemi kotu ta yi masa sassauci

- Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin zaman gidan wakafi na watanni 5 ko kuma biyan tara na N13,000

Wata Kotun Gunduma ta 1, Karu, ta yanke wa wani mutun dan shekaru 19, mai suna Sadiq Abdullahi, hukuncin dauri na tsawon watanni 5 don ya saci kayan makwabcinsa da darajarsu zata kai N10,500.

Kotu da daure shi na watanni 5 bayan an same shi da laifin yiwa makwabcin sa sata

Kotu da daure shi na watanni 5 bayan an same shi da laifin yiwa makwabcin sa sata

Abdullahi, yana zama a Gamji Road, a kauyen Karu, ya amince da laifuka biyu da ake tuhumarsa da aikatawa na cin amana da kuma zamba, ya kuma nemi da a sassauta masa hukunci kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Za'a kammala tashan jirgin ruwa na kan tudu na Funtua a watan Mayu

Alkalin Hassan Ishaq, a shari’ar ya bama wanda ake zargin damar ya biya tara ta N13,000.

Mai gabatar da kara Vincent Osiji, ya fadawa Kotu cewa wani mai suna Yahaya Mohammed wanda suke zaune a wuri daya wanda akayi wa satar ne kawo karar a ofishin ‘Yan Sanda na Karu.

Osiji ya ce wanda ake tuhumar ya shigar masu gida ne cikin tsakiyar dare a ranar 23, ga watan Fabrairu in da ya satar masu kayan da kudinsu zasu kai kimanin N10,500, ya kuma sayar wa wani mai suna Nasiru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel