Nigerian news All categories All tags
Faduwa gaba asarar namiji: Shugaban Koriya Ta Arewa ya bayar da sharadin rabuwa da makaman sa

Faduwa gaba asarar namiji: Shugaban Koriya Ta Arewa ya bayar da sharadin rabuwa da makaman sa

Babbar abokiyar hamayyar Koriya ta arewa kuma makwafciyar ta watau Koriya Ta Kudu ta ce shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayar da hasken cewa zai so hawa teburin tattaunawa a kan rabuwa da makaman nukiliya idan za a ba shi tabbacin tsaron kasarsa.

Kasar ta Koriya Ta Kudun ta ce dai an tattauna wannan batun ne a yayin da wasu wakilan ta suka gana da shugaban na Koriya Ta Arewa mai suna Kim Jong-un a birnin Pyongyang babban birnin kasar a ranar Litinin din da ta gabata.

Faduwa gaba asarar namiji: Shugaban Koriya Ta Arewa ya bayar da sharadin rabuwa da makaman sa

Faduwa gaba asarar namiji: Shugaban Koriya Ta Arewa ya bayar da sharadin rabuwa da makaman sa

KU KARANTA: Wanda aka haifa a Zamfara ya zama Sanata a Italiya

Legit.ng haka zalika ta samu cewa gwamnatin ta Kasar ta Koriya Ta Kudun a birnin Seoul ta kuma bayyana cewa Koriya Ta Arewa ta ce a shirye take ta gudanar da tattaunawa da Amurka game da dakatar da gwaje-gwajenta na makamai masu linzami da na nukiliya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a can baya kasar ta Koriya Ta Arewa ta sha yin fatali da alkawuran da take dauka na dakatar da shirin nukiliyarta.

A wani labarin kuma, Wani mutum mai suna Toni Iwobi wanda dan asalin kasar Najeriya ne da aka haifa a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya ya samu nasarar zama dan majalisar dattijai a kasar Italiya dake tarayyar turai a zaben da ya gudana.

Shi dai Mista Iwobi kamar yadda muka samu ya tafi kasar ta Italiya ne tun shekara ta 1970 inda kuma ya shiga harkar siyasar kasar kafin daga bisani ya samu mukamin jami'in 'yan kasar waje na jam'iyyar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel