Nigerian news All categories All tags
Abin da za mu fadawa Shugaba Buhari idan ya zo Jihar Ribas - Gwamnatin Wike

Abin da za mu fadawa Shugaba Buhari idan ya zo Jihar Ribas - Gwamnatin Wike

- Ana sa ran cewa Shugaban Kasa Buhari zai kai ziyara Ribas kwanan nan

- Gwamnatin Jihar ta Ribas tace ta shirya tarbar Shugaban kasa Buhari

- Gwamnatin Wike tace sa ga fayyacewa Shugaban kasar matsololin Jihar

A cikin 'yan kwanakin nan ne Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai kai ziyara wasu Jihohin kasar da rikici ya kaure. Daga cikin wadannan Jihohi akwai Ribas wanda ke karkashin Jam'iyyar adawa ta PDP.

Abin da za mu fadawa Shugaba Buhari idan ya zo Jihar Ribas - Gwamnatin Wike

Shugaban kasa Buhari tare da Gwamnan Jihar Taraba

Gwamnatin Jihar Ribas ta bayyana abin da za tayi wa Shugaban kasa Buhari idan ya kawo mata ziyara. Kwamishinan yada labarai na Jihar Emma Okah yace abu ne mai kyau a ce Shugaban kasa ya ziyarci Jihar don kuwa shi na kowa ne.

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bikin 'yancin kan kasar Ghana

Kwamishinan ke cewa Jihar za tayi amfani da wannan dama ta bayyanawa Shugaban kasa Buhari yadda Gwamnatin Tarayya ta APC tayi watsi da su bayan hawan ta mulki da kuma irin kalubalen da su ke samu musamman a harkar tsaro.

Emma Okah ke cewa za su fadawa Shugaban kasar cewa ba su samun hadin-kan da ya kamata daga Jami'an 'Yan Sanda kuma ana kokarin hada kai da Jami'an tsaron wajen murdewa Jam'iyyar Shugaban kasar ta APC zabe mai zuwa na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel