Nigerian news All categories All tags
Fayose ya ajiye kudirin takarar shugabancin kasa, yana hararar kujerar Osinbajo

Fayose ya ajiye kudirin takarar shugabancin kasa, yana hararar kujerar Osinbajo

Hasashe sun nuna cewa ga dukkan alamu Gwamnaa Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya ajiye kudirinsa na takarar shugabancin kasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamnan wanda wa’adin mulkinsa na shekara hudu zai kare a wannan shekarar, ya nuna kudirinsa a watan Satumban 2017 a Abuja.

Tun lokacin, ba’a ji wani abu daga gareshi akan kudirin nasa ba.

Wani mamba na kwamitin amintattun jam’iyyar yace gwamnan jihar Ekitin ya ga cewa kudirinsa na takarar shugabanci ba mai yiwuwa bane.

Ya kara da cewa, a wani taron da akayi kwanan nan, Fayose na aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa PDP ta gabatar da wani gawurtaccen dan takara daga Arewa wanda zai iya kayar da duk wani dan takara da zai fito daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Fayose ya ajiye kudirin takarar shugabancin kasa, yana hararar kujerar Osinbajo

Fayose ya ajiye kudirin takarar shugabancin kasa, yana hararar kujerar Osinbajo

Akan makomar siyasar gwamnan, yace a yanzu haka gwamnan na neman kujerar mataimakin gwamna a jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Abin da za mu fadawa Shugaba Buhari idan ya zo Jihar Ribas - Gwamnatin Wike

Da yake magana da jaridar daily independent, Lere Olayinka, hadimin Fayose, ya karyata rahoton cewa shugabansa ya dakatar da kudirinsa.

Olayinka, wanda yace har yanzu Fayose na nan akan bakarsa, ya bayyana cewa tunda Fayose ya bayyanawa jama’a kudirinsa, idan ya janye zai sake fada masu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel