Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Matasan Najeriya sun tsaida Gwamna Dankwambo takarar shugaban kasa

Zaben 2019: Matasan Najeriya sun tsaida Gwamna Dankwambo takarar shugaban kasa

Wata kungiyar matasan jam'iyyar adawa ta kasa watau Concerned Peoples Democratic Party Youths a turance sun fitar da gwamnan jihar Gombe takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar matasan Malam Sani Bello ya fitar dauke da sa hannun sa a jiya Talata.

Zaben 2019: Matasan Najeriya sun tsaida Gwamna Dankwambo takarar shugaban kasa

Zaben 2019: Matasan Najeriya sun tsaida Gwamna Dankwambo takarar shugaban kasa

KU KARANTA: Ziyarar Filato: Ma'aikata sun sun samu hutu don tarbar Buhari

Legit.ng ta samu cewa kungiyar ta bayyana gwamnan da yanzu haka yake da shekaru 55 a duniya kacal a matsayin wanda yafi kowa cancanta da ya shugabancin kasar nan musamman ma saboda irin yadda aka ga kamun ludayin sa a jihar ta Gombe.

A wani labarin kuma, Wani mutum mai suna Toni Iwobi wanda dan asalin kasar Najeriya ne da aka haifa a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Najeriya ya samu nasarar zama dan majalisar dattijai a kasar Italiya dake tarayyar turai a zaben da ya gudana.

Shi dai Mista Iwobi kamar yadda muka samu ya tafi kasar ta Italiya ne tun shekara ta 1970 inda kuma ya shiga harkar siyasar kasar kafin daga bisani ya samu mukamin jami'in 'yan kasar waje na jam'iyyar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel