Nigerian news All categories All tags
Badakalar fansho: Majalisar wakillai ta aikawa Okonjo-Iweala da takardar sammaci

Badakalar fansho: Majalisar wakillai ta aikawa Okonjo-Iweala da takardar sammaci

Wani kwamitin dake binciken kwa-kwaf a kan harkokin kasa na majalisar wakillai ya aikewa da uwar gida Okojo-Iweala dake zaman tsohuwar shugabar kwamitin gyara da garambawul na harkokin 'yan fanshon kasa da sammaci bisa zargin almundahana.

Majiyar mu ta Premium Times haka zalika ta ruwaito cewa majalisar ta wakilai ta aika mata da sammacin ne don ta zo tayi masu karin haske game da sauye-sauyen da ta jagoranci kawowa a harkar ta fansho tun daga shekarar 2010.

Badakalar fansho: Majalisar wakillai ta aikawa Okonjo-Iweala da takardar sammaci

Badakalar fansho: Majalisar wakillai ta aikawa Okonjo-Iweala da takardar sammaci

KU KARANTA: Zazzabin Lassa ya yi barna a jihar Bauchi

Legit.ng ta samu haka zalika cewa sauran wadanda majalisar wakilan suka gayyata sun hada da shugabar ma'aikata Winifred Oyo-Ita, shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emiefele da dai sauran su.

A wani labarin kuma, 'Yan majalisar wakillan Najeriya sun bayyana matsayar su biyo bayan kwamacalar zaben kananan yara da ake zargin an tafka a zaben kananan hukumomin da ya gabata a jihar a kwanakin baya inda suka bayyana cewa za su binciki lamarin.

Daga nan ne ma kuma dai sai majalisar suka dora alhakin binciken ga kwamitin majalisar dake kula da harkokin zabe da jam'iyyu domin farawa sannan kuma ya kawo wasu rahoto cikin sati 5.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel