Nigerian news All categories All tags
Sanata Stella Oduah ta ajiye fasfon ta a hannun Hukumar EFCC

Sanata Stella Oduah ta ajiye fasfon ta a hannun Hukumar EFCC

- EFCC na zargin Stella Oduah da karkatar da wasu makudan Biliyoyin kudi

- Ana kokarin kama Ministar da laifin lashe kudin aiki a wasu filayen jirgi 22

- Yanzu haka Hukumar dai ta karbe takurdun Sanatan domin hana ta tserewa

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na cigaba da binciken wata tsohuwar Ministan Najeriya da ake zargi da yi gana da Biliyan 3.9 cikin wasu kudin Gwamnati. Yanzu dai an karbe takurdun wannan mata.

Sanata Stella Oduah ta ajiye fasfon ta a hannun Hukumar EFCC

Ibrahim Magu ya taso Sanata Stella Oduah a gaba

EFCC na binciken Sanata Stella Oduah wanda ta rike Ministan sufurin jirgin sama na kasar nan a lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Yanzu haka dai Hukumar ta rike fasfon tsohuwar Ministar bayan wasu tambayoyi.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya cika shekaru 81 a Duniya

Idan ba ku manta ba a wancan makon, EFCC ta tsare Stella Oduah na sama da awanni 10 inda ta sha matsa kan kudin da ake zargi ta karkatar har sama da Biliyam 3.9 cikin Naira Biliyan 9.4 da aka ware domin inganta tsaro a filayen jirgi.

Tun a lokacin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan babban Lauyan da ke kare hakkin Jama’a a kasar nan Femi Falana yam aka Ministar a Kotu bayan ta barnatar da har sama da Miliyan 255 wajen sayen wasu motoci 2 rak na kirar BMW.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel