Nigerian news All categories All tags
Bikin 'yancin kai: Shugaba Muhammadu Buhari yayi jawabi a Ghana

Bikin 'yancin kai: Shugaba Muhammadu Buhari yayi jawabi a Ghana

- Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bikin 'yancin kan kasar Ghana

- Shugaban na Najeriya ne babban bakon da aka gayyata daga Kasar waje

- Muhammadu Buhari yayi wani jawabin da ya burge Jama’a a wajen taron

A makon nan ne Kasar Ghana ta cika shekaru 61 da samu 'yancin kai a Duniya. Asali ma Shugaba Buhari ne babban bakon da aka gayyata zuwa bikin da aka yi a babban filin taron 'yancin kai na kasar da ke babban Birnin Accra na kasar.

Bikin 'yancin kai: Shugaba Muhammadu Buhari yayi jawabi a Ghana

Shugaba Muhammadu Buhari a bikin 'Yancin kan kasar Ghana 61

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki su na cikin Shugabannin da su ka halarci wannan biki. Bayan taron ne Shugaban kasar ya hau jirgin filin jirgi na Kotoka a Kasar ya dawo gida.

KU KARANTA: Mun yi kokari a harkar tsaro a Najeriya - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a jawabin da yayi a taron ya tuno da maganar tsohon Shugaban kasar Ghana Kwame Nkurmah wanda yace duk wadanda ke duba nisan da mu kayi a Afrika, zai yi kyau kuma su duba daga inda mu ka fara.

Idan ba a manta ba dai Shugaban kasar yana zagayen Jihohin da rikicin tsaro ya afka masu a gida inda kuma yace har abokan hamayyar su sun san cewa Gwamnatin sa tayi namijin kokari a kan sha'anin inganta tsaro a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel