Nigerian news All categories All tags
Ma'aikatan jami'ar ABU sun janye yajin aiki

Ma'aikatan jami'ar ABU sun janye yajin aiki

- Tsawon watanni uku kenan ma'aikatan jami'o'in kasar nan su ka shude cikin yajin aiki

- An samu rudani tsakanin 'ya'yan kungiyar ma'aikatan dangane da batun janye yajin aikin

- Daliban jami'ar sun bayyana farincikinsu da janye yajin aikin

Kungiyar ma'aikatan jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria sun bayyana cewar sun janye yajin aikin da su ka shiga watanni uku da su ka wuce.

Shugaban kungiyar reshen jami'ar, Abdulrauf Bello, ya sanar da hakan bayan kammala taron kungiyar reshen jami'ar.

Ma'aikatan jami'ar ABU sun janye yajin aiki

Ma'aikatan jami'ar ABU sun janye yajin aiki

"Ina umarta dukkan 'ya'yan kungiyar mu da su gaggauta komawa bakin aiki. Tsawon watanni uku kenan muna yajin aiki amma aikin jami'a bai tsaya ba. Saboda haka yajin aikin bashi da wani amfani," a cewar Abdulrauf.

KU KARANTA: Da duminsa: Jirgin yakin soji dauke da dakaru 32 ya yi hatsari, dukkan su sun mutu

Sai dai wannan umarni na kungiyar ma'aikatan jami'ar ta ABU ta kawo rudani da rabuwar kayuwa a tsakanin 'ya'yan kungiyar domin Jim kadan bayan sanarwar janye yajin aikin, Malam Alfa Gimba, tsohon shugaban kungiyar ma'aikatan reshen jam'iar ya fito yana mai bayyana cewar Abdulrauf ba shi da ikon bayar da sanarwar janye yajin aikin domin ba mamba ba ne a kungiyar.

Gimba ya kara da cewar tuni kungiyar ta tsige shi daga shugabancin kungiyar kuma hatta kotu ta ki ta yarda da bukatar mayar da shi, a saboda haka ba shi da ikon bayar da sanarwar janye yajin aikin.

Wasu dalibai da jaridar Daily Trust tayi hira da su sun bayyana jin dadinsu bisa janye yajin aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel