Nigerian news All categories All tags
NNPC: Najeriya tana sarrafa kowanne gangar mai akan Dala 20

NNPC: Najeriya tana sarrafa kowanne gangar mai akan Dala 20

- Najeriya na sarrafa gangar mai akan dala 20

- Dr. Maikanti Baru ya ce burin gwamnatin Najeriya shine sarrafa gangar man ya dawo dala 15

-Gwamnatin tarayya ta ce zata bayyana sunayen kamfanonin da zasu yi aikin gyaran matatun man fetur a kasar nan

NNPC: Najeriya tana sarrafa kowanne gangar mai akan Dala 20

NNPC: Najeriya tana sarrafa kowanne gangar mai akan Dala 20

Manajan Darekta na hukumar NNPC, Dr. Maikanti Baru ya ce kamfanin ya rage kudin sarrafa man fetur zuwa dala 20 ko wacce ganga.

Baru ya bayyana hakan a wurin wani bikin bude cinikayyar fasaha na 2018 wanda ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Abuja ta shirya a jiya.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta na gina gidaje masu araha ga al'umma

Rage kudin sarrafa man shine zai karawa gwamnatin kudin da take samu daga bangaren man fetur. Burin mu shine ya dawo dala 15, kuma zamuyi kokari muyi aiki akan hakan. In ji shi.

Gwamnatin tarayya ta ce zata bayyana sunayen kamfanonin da zasu yi aikin gyaran matatun man fetur din nan ba da jimawa ba.

Baru ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da bada aikin bututun mai daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK), akan kudi dala biliyan 2.8.

Ya ce: "Wadanda aka bawa kwangilar aikin bututun gas din, zasu zo da kayan aikin su suyi aikin bututun a gaban mu," sannan ya fadi yanda aikin bututun zai amfani 'yan kwangilar Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel