Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin tarayya ta amince da biyan N650bn na tallafin man fetur

Gwamnatin tarayya ta amince da biyan N650bn na tallafin man fetur

Hasashe sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta amince da biyan naira biliyan 650 kudin tallafi ga masu rijiyar mai da masu saida mai.

A cewar wata sanarwa daga kungiyar masu rijiyar mai da masu saida mai wato Depot and Petroleum Products Marketers Association of Nigeria (DAPPMA), dauke da sa hannun Mista Dapo Abiodun, shugaban kungiyar da Olufemi Adewole, sakataren kungiyar a Lagas, gwamnatin tarayya ta ba masu dillancin man fetur tabbacin biyan kudin inda take jiran yardan majalisar dokokin kasar.

Yan kasuwan na sanya ran cewa za a amince da kudirin biyan ba tare da daukar dogon lokaci ba.

Gwamnatin tarayya ta amince da biyan N650bn na tallafin man fetur

Gwamnatin tarayya ta amince da biyan N650bn na tallafin man fetur

Sakamakon haka, hukumar DAPPMA/MOMAN, sun janye zance wa’adin kwanaki 14 da suka bayar sannan kuma sun roki ma’aikatansuna kungiyoyi daban-daban da suyi hakuri yayinda akee jiran amincewar majalisar doki.

KU KARANTA KUMA: Buhari ne keda kasa, yana iya ziyara a ko wani lokaci - Ortom

DAPPMA ta bukaci mambobin da su tabbatar da cewa ba’a janye hankulasu daga rarraba man fetur a fadin kasar ba.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne uban kasa sannan kuma yana iya ziyartan ko wani jiha a duk lokacin da ya yi ra’ayi.

Gwamna Ortom wanda yayi magana ta baki sakataren labaransa, Terver Akase ya bayyana cewa Benue na daga cikin yankin Najeriya sannan kuma yana iya ziyartan su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel