Labari da duminsa: Majalisa ta umurci Ministan Zirga-Zirgan Jiragen Sama ya bayyana gaban ta

Labari da duminsa: Majalisa ta umurci Ministan Zirga-Zirgan Jiragen Sama ya bayyana gaban ta

- Majalisan Dattawa ta aike da gayyata ga Ministan filayen jiragen sama, Hadi Sirika bisa matsalolin da ke tasowa a filayen jiragen sama cikin kwanakin nan

- Dan majalisa mai wakiltan gabashin Legas, Sanata Gbenga ya bayyana damuwar sa kan yadda ake samun mishkila da yawa a filayen jiragen saman

- Majalisar tana zargin cewa akawai ma'aikatan da basu gudanar da aikin su yadda ya kamata shi yasa ake samun ire-iren wannann matsalolin

Majalisar Dattawa ta bukaci Ministan filin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana gaban majalisar don yin bayyani game da matsalolin da ake samu a filayen jirgin saman cikin yan kwanakin nan da ke barzana ga rayuwan al'umma.

Labari da duminsa: Majalisa ta umurci Ministan jiragen Sama ya bayyana gaban ta

Labari da duminsa: Majalisa ta umurci Ministan jiragen Sama ya bayyana gaban ta

Kamar yadda muka sama daga Channels tv, Dan majalisar mai wakiltan gabashin Legas, Sanata Gbenga Ashafa ya lura cewa an samu matsaloli biyu a filayen jirgin saman a watan Fabrairun 2018.

KU KARANTA: 'Yan daba sun kai hari gidajen shugabanin PDP a jihar Kogi

Daya daga cikin su ya faru ne yayin da wata jirgi mallakin Dana Airline ta ketare titin saukan jirgin yayin da ta sauka a filin sauka jirage na Port Harcourt bayan ta kwaso fasinjoji daga babban birnin Tarayya Abuja.

Sai dai Janar Manaja na sashin ayyukan na hukumar ta filayen jiragen sama na kasa FAAN, Henrietta Yakubu ta yi bayyani inda ta ce, "Ana tsamanin ruwan sama da iski mai karfi da ya faru rannar ne ya haifar a garin na Port Harcourt kuma babu wanda ya rasu sakamakon lamarin."

Amma duk da hakan, Dan Majalisan ya nuna damuwa bisa yadda ake kara samun matsaloli a filayen tashin jiragen saman wanda ya ce alama ce da ke nuna cewa wasu ma'aikatan ba su gudanar da aikin su yadda ya dace kafin su bawa jirgi umurnn tashi ko kuma sauka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel