Buhari ya ki aikawa Obasanjo sakon murnar cika shekaru 81 da haihuwa

Buhari ya ki aikawa Obasanjo sakon murnar cika shekaru 81 da haihuwa

- Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun ya cika shekaru 81 da haihuwa

- shugaba Buhari ya ki aikawa Obasanjo sakon murnar cika shekaru 81 da haihuwa

A ranar litinin 5 ga watan Mayu, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya cika shekaru 81 da haihuwa, 'yan uwa da abokan arziki da ‘yan siyasa sun aikawa masa da sakon murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

A cikin manyan mutanen da suka aika wa Oabsanjo sakon murna zagayowar ranar haihuwar sa akwai tsohon mataikin shugaban kasa, Atiku Abubakar, shugaban majalissar Dattawa, DaktaBukola Saraki, Sanata David Mark, gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun da mambobin jam’iyyar PDP da APC.

Buhari ya ki aikawa Obasanjo sakon murnar cika shekaru 81 da haihuwa

Buhari ya ki aikawa Obasanjo sakon murnar cika shekaru 81 da haihuwa

A wannan karon, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kadai bai aika wa Obasanjo sakon taya shi murna ranar zagoyawar haihauwar sa ba.

Har yaznu babu wanda yasan dalilin da ya sa shugaba Buhari bai aika wa Obasanjo sakon murnar cika shekaru 81 da haihuwa.

KU KARANTA : Masu bincike sun gano sabuwar maganin cutar kanjamau

Legit.ng ta samu rahoton cewa, ofishin shugaban kasa, yana da jami’ai na musamman da aikin su shine aikawa manya ‘yan Najeriya sakon taya su murnar zagayowar ranar haihuwar su.

Kamar wadda aka aikawa tsohon Cocin kungiyar kungiyar kwallon kafa ta kasa, Adegboye Onigbinde, da ya cika shekaru 80 da haihuwa. A ranar Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel