Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin Tarayya ta na gina gidaje masu araha ga al'umma

Gwamnatin Tarayya ta na gina gidaje masu araha ga al'umma

- Gwamnatin tarayya ta na gina gidaje masu araha ga ‘yan Najeriya a fadin kasar nan

- Mai kula da ayyukan gwamnatin tarayya a jihar, Mista Bob Isiki, yace gidajen sun hada da masu dakuna 2 da kuma masu dakuna 3

- An shawarci gwamnatin da ta bada himma wurin cigaba da wadannan kyawawan ayyuka da takeyi na taimaka wa mutanen Najeriya da wuraren zama

Gwamnatin Tarayya ta na gina gidaje masu araha ga al'umma

Gwamnatin Tarayya ta na gina gidaje masu araha ga al'umma

Gwamnatin tarayya ta na gina gidaje masu araha ga ‘yan Najeriya a fadin kasar nan a karkashin ayyukan ma’aikatar kula da gidaje, in ji Ministan ayyuka, wuta da gidaje na Najeriya, Babatunde Fashola.

DUBA WANNAN: Iska mai karfi ta yi sanadiyyar jefa miliyoyin jama'a cikin tashin hankali

Ministan yayi bayanin ne a ranar Litinin a garin Kaduna lokacin da yake duba ayyukan ginin wasu gidaje guda 80, an kawo shirin gina gidajen ne domin ya mayar da gurbin rashin gidajen da ake fama dashi a kasar nan. Wakilin ministan, Darakta na arewa maso yamma Highways, Mista Olalekan Busari, ya bayyana cewa ‘yan kwangila 20 aka bawa kula da aikin a Kaduna.

Mai kula da ayyukan gwamnatin tarayya a jihar, Mista Bob Isiki, yace gidajen sun hada da masu dakuna 2 da kuma masu dakuna 3, wanda a yanzu haka an kai kashi 75 cikin dari na kammaluwar aikin.

Aishatu Tisha, shugabar wakilan aikin na tarayya, ta ce, ayyuka da akeyi a fadin kasar zai taimakawa matasa da kuma ‘yan kasuwa wadan da ake sayen kayan aiki daga wurin su.

Mataimakin shugaban injiniyoyin na yankin jihar kaduna, Nasiru Dalhatu, yayi godiya ga gwamnatin tarayya na ayyukan da takeyi musamman ma wajen tallafawa kana nan magina, ya kuma yi godiya ga ‘yan kwangila bisa ga ingattacen aikin da suke yi a wurin ginin.

Dalhatu ya shawarci gwamnatin da ta bada himma wurin cigaba da wadannan kyawawan ayyuka da takeyi na taimaka wa mutanen Najeriya da wuraren zama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel