'Yan daba sun kai hari gidajen shugabanin PDP a jihar Kogi

'Yan daba sun kai hari gidajen shugabanin PDP a jihar Kogi

- Yan daba dauke da bindigogi da makamai daban-daban sun kai hari gidan dan majalisa mai wakiltan Kogi ta tsakiya

- Sanatan ya yi ikirarin cewa yan jam'iyyar adawa na jihar ne suka turo yan daban don su cin musu zarafi da kuma razana su

- Yan daban kuma sun kai hari gidan shugaban PDP na jihar, Mallam Adinoyi Aroke da kuma gidajen wasu kusoshin jam'iyyar duk dai a jihar

An kai hari a gidan na shugaban PDP da ke kauyensu na Okene, da kuma gidan tsohon dan majilissar wakilai, Alh. Abdulkarem Salihu, tare da wasu gidajen mutune uku daga jam'iyyar ta PDP a kauyukan na Okene, Okehi da Adavi duk an kai harin.

Majiya da ta fito daga wurin Sanatan ta bayyana cewa anyi asarar dukiya ta miliyoyin kudi. Wata majiyar tamu ta bayyana mana cewa 'yan daban sama da mutune 50 ne suka kai hari a gidan na Ogembe wanda ke kauyen Obehira, Okene local government a jihar, in da suka lalata dukiya ta miliyoyin kudi.

'Yan daba sun kai hari gidan shugaban PDP a jihar Kogi

'Yan daba sun kai hari gidan shugaban PDP a jihar Kogi

A wani jawabi da Dan Majalissar ya yi, ya bayyana cewa 'yan ta'addan kwararru ne wurin cin mutunci da cin zarafi da kisan mutane wanda aka sanya su daga jam'iyyar adawa cikin jawabin shi a ranar Litinin, ya kara da yin kira ga jami'an tsaro da suyi kokari su kama kuma su hukunta wadanbda suka aikata wannan mugun aiki.

KU KARANTA: Wata mace ta damfari wani kamfanin jigilar mahajjata kudi N23.9m

"Ba muna kira ga jami'an tsaro da su kamasu ba kadai munaso su gurfanar dasu a gaban shari'a don muna da isassun shaidun da zamu gabatar a gaban ta a za'a hukunta su, bayan yunkurin da sukayi na hana mu yin taron wanda matasan mu da jami'an tsaro suka jajirce wurin hana tashin hankalin da ganin cewa anyi taron lafiya" inji shi

Lokacin da yake magana da 'yan jarida, ya ce an kai hari a gidan nasa inda aka lalata masa motoci 3, sai da jami'an tsaro suka iso wurin sannan aka samu matasan suka haura ta katanga suka ruga.

A halin yanzu babu wani kwakwaran bayani da ya fito daga wurin jami'an tsaro na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel