Nigerian news All categories All tags
Wata mace ta damfari wani kamfanin jigilar mahajjata kudi N23.9m

Wata mace ta damfari wani kamfanin jigilar mahajjata kudi N23.9m

- Hukumar Yan Sanda tayi kama wata mace wadda ta damfari wani kamfanin jigilar maniyyata kudi N23.9m

- Matar mai suna Mrs. Edward Akinwunmi Olamide ta hada kai ne da wasu wajen damfarar kamfanin mai suna Alhujaaj International Umrah and Hajj Services

- Sai dai wanda ake tuhuma ta musanta aikita laifin, hakan yasa aka bayar da ita beli kuma aka dage sauraron karar

Hukumar Yan Sanda a jihar Legas ta kama wata da laifin damfarar hukumar mahajjata kimanin kudi N23.9m. ‘Yar damfarar mai suna, Mrs. Edward Akinwunmi Olamide, ta gurfana a gaban kotun majisatre na unguwar Ebute-Metta , a jihar Legas, bisa laifin yaudara da kuma sata.

Wata mace ta damfari hukumar jigillar Mahajjata kudi N23.9m

Wata mace ta damfari hukumar jigillar Mahajjata kudi N23.9m

Jami’am ‘yan sanda na SCIID, Panti-Yaba, Legas, sun bayyana cewa matar mai shekaru 32 tare da wasu da basu kaiga shiga hannu ba, sun hada kai sun damfari hukumar mai suna Alhujaaj International Umrah and Hajj Service a ranar 30 ga watan Nuwamba, shekarar 2017.

KU KARANTA: 'Dan kunar bakin wake ya kashe jami'an tsaro 3, ya kuma raunana mutum 17 a Borno

Laifukan daga bakin mai gabatar da kara Inspector Chinnalu Uwadione, sun sabawa shari’a a sashe 411 da 287(7) na dokar Criminal law Cap. Ch. C17, Vol.3, Law na jihar Legas a Najeriya, shekara ta 2015.

Bayan ta nemi beli, babbar mai gabatar da karar, Mrs. Oluwayemisi Adelaja, ta yarda da bada ta belin akan kudi N2m da kuma mutune biyu da zasu biya mata.

Kotun dai ta dage shari’ar zuwa 28 ga watan Maris, domin cigaba, a kuma tsare mai laifin a gidan wakafi har zuwa lokacin da ta cika sharadun belin na ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel