Nigerian news All categories All tags
Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

- Adadin mutanen da aka kashe a Taraba sun fi adadin mutanen da aka kashe a jhar Benuwe da Taraba

- Shugaba Buhari ya jajantawa mutanen da rikicin Mambila a jihar Taraba ya afka da su

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa adadin mutanen da aka kashe a rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a yankin Mambilla dake jihar Taraba, sun fi adadin mutanen da aka kashe a jihar Benuwe da Zamfara.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a brinin Jalingo dake jihar Taraba, a lokacin da yake tattaunawa da Fulani da sauran kabilun yankin.

Buhari yay a ziyarci jihar Taraba ne domin jajantawa mutaen da rikicin tsakanin manoma da makiyaya ya afka da su inda y ace zuba da jinni dan Adam laifin ne mai matukar muni.

Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

Rikicin Taraba ya fi na Benuwe da Zamfara muni – Buhari

Ya kuma kara da cewa samar da zaman lafiya da tsaro ba aikin gwamnati ba ce ita kadai, sai an samu hadin kan Jama’a.

KU KARANTA : Masu bincike sun gano sabuwar maganin cutar kanjamau

Daga nan sai ya yi roko da cewa a rika tabbatarwa an yi adalci ga kowane bangare, ya na mai cewa a tabbatar da an zakulo wadanda suka yi kisa an hukunta su.

Daga karshe gwamnan jihar Taraba, Mista Ishaku Darius, ya gode wa, Shugaba Buhari, tare da tabbatar masa cewa gwamnatin sa za ta yi iyakar kokarin ta wajen ganin an dawo da zaman lafiya a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel