Nigerian news All categories All tags
Uwargidan shugaba Buhari ta karbi bakuncin shugabannin mata na jam'iyyar APC

Uwargidan shugaba Buhari ta karbi bakuncin shugabannin mata na jam'iyyar APC

- Uwargidan shugaba Buhari ta karbi bakuncin shugabannin mata na jam'iyyar APC

- Ta bukaci su fito su zabi shugabanni masu riko da gaskiya da cika alkawari da zasu kare mutuncin su

- Uwargidan shugaban kasar bata ambaci sunan maigidanta, shugaba Buhari, ba yayin taron

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara karatowa, jam'iyyu da 'yan siyasa na cigaba da yin taro da tuntuba domin daure kayan su a gindin kaba.

A jiya ne shugabannin mata na jam'iyyar APC su ka ziyarci mai dakin shugaban kasa, Aisha Buhari, a gidan gwamnati.

Uwargidan shugaba Buhari ta karbi bakuncin shugabannin mata na jam'iyyar APC

Uwargidan shugaba Buhari ta karbi bakuncin shugabannin mata na jam'iyyar APC

Bayan shugabannin jam'iyyar, taron ya samu halartar uwar gidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, matar gwamnan jihar Sokoto, Hajiya Mairo Tambuwal, da mataimakiyar shugabar matan jam'iyyar APC, Tina Adike.

KU KARANTA: Assha: An kama wani mahaifi da dansa da ke sayar wa daliban frimare miyagun kwayoyi

Yayin taron, Aisha Buhari ta yi kira ga shugabannin mata na jam'iyyar da su goyi bayan 'yan takara dake da kwarewa da kuma riko da gaskiya da cika alkawari.

Abin mamakin shine yadda Aisha bata ambaci sunan maigidanta ba ko kira ga matan da su goyi bayansa ba.

Sulaiman Haruna, darektan yada labarai a ofishin Aisha Buhari, ya ce ziyarar da Shugabannin matan su ka kai ta ban girma ce kawai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel