Karin Albashi: Muna yin iya bakin kokarin mu domin ganin an samu karin albashi - Shugaban Kungiyar Kwadago

Karin Albashi: Muna yin iya bakin kokarin mu domin ganin an samu karin albashi - Shugaban Kungiyar Kwadago

- Dokta Chris Ngige, ya tabbatar wa da ma'aikatan Najeriya cewa gwamnati tana nan tana iya bakin kokarin ta domin ganin an gabatar da sabon tsari na karin albashi

- Shugaban ya bayyana cewa, kwamitin da aka kafa domin yin tsare-tsaren karin albashin zata gabatarwa da majalisar dattijai sakamako na karshe a cikin wannan shekarar

Karin Albashi: Muna yin iya bakin kokarin mu domin ganin an samu karin albashi - Shugaban Kungiyar Kwadago

Karin Albashi: Muna yin iya bakin kokarin mu domin ganin an samu karin albashi - Shugaban Kungiyar Kwadago

A ranar Litinin din nan ne shugaban kungiyar kwadago na kasa, Dokta Chris Ngige, ya tabbatar wa da ma'aikatan Najeriya cewa gwamnati tana nan tana iya bakin kokarin ta domin ganin an gabatar da sabon tsari na karin albashi. Ya ce gwamnati ta kafa kwamiti, wanda a yanzu haka kwamitin tana nan tana aiki domin samo mafita.

DUBA WANNAN: Ya kamata gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa - Edwin Clark

Mista Ngige ya bada tabbacin hakan yayin da yake magana da manema labarai, jim kadan bayan fitowar shi daga wurin taron rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi a jihar Edo. Inda jam'iyyar APC mai mulki ta lashe zaben.

Shugaban ya bayyana cewa, kwamitin da aka kafa domin yin tsare-tsaren karin albashin zata gabatarwa da majalisar dattijai sakamako na karshe a cikin wannan shekarar.

Ya ce "Wannan wani tsari ne na kasa wanda ta tsara akan duk bayan shekaru biyar sai an sake gyara akan yanayin albashin ma'aikata. "Sannan ya kara da cewa kwamitin zata yanke hukunci game da yanda sabon tsarin albashin zai kasance.

Sannan ya yabawa gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki, bisa kokarin da yayi akan sabbin shugabannin kananan hukumomin, sannan kuma ya shawarci shugabannin kananan hukumomin da su yi kokari wurin ganin sunyi wa talakawan su aiki yanda ya kamata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel