Nigerian news All categories All tags
Kotu ta bawa Hukumar EFCC umarnin kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai , Mista Ogor

Kotu ta bawa Hukumar EFCC umarnin kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai , Mista Ogor

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta samu umarnin daga kotu na kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai

- Ana zargin shi da bada ayyuka wadanda har yanzu ba ayi su ba

- Hukumar ta bukaci daya bayyana a gabanta amma yayi watsi da gayyatar

Kotu ta bawa Hukumar EFCC umarnin kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai , Mista Ogor

Kotu ta bawa Hukumar EFCC umarnin kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai , Mista Ogor

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa ta karbi takarda daga kotu, don kama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Leo Ogor, akan zargin shi da ake da kin gudanar da ayyuka guda 20 da aka bashi. A kowanne lokaci hukumar zata iya zuwa domin kamo shi, bayan da ake zargin shi da kin bayyana a gaban hukumar domin bincike.

An ce ayyukana da aka bashin sun kai na kimanin naira miliyan 500, wanda aka ba da su ga kamfanoni da suke da dangantaka da shi Mista Ogor.

Amma har yanzu hukumar yaki da cin hanci da rashawar taki ta janye dokar dakatar da kudin naira miliyan 116 wanda suke cikin 5 daga cikin kamfanoni 6 da shi Mista Ogor ya mallaka, wanda kuma ake zargin sune suka karbi kwangilar ayyukan daga wasu hukomomi da nufin cewar zasu gabatar da aikin.

DUBA WANNAN: Majalisar wakilai tana tuhumar kamfanoni 31 bisa zargin su da cin hanci da rashawa

A cikin laifukan da ake zargin Mista Ogor da aikata wa akwai kudi naira miliyan 318 na kwamitin Niger Delta Development (NDDC); sai ayyuka 20 da ake zargin shi da karba amma bai aikata su ba, aikin hukummar ilimi (UBEC), aikin kwamitin kula da yan gudun hijira, da dai sauran su.

Bincike ya nuna cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta karbo takarda daga kotu, dake nuni da cewa a kama Mista Ogor, bayan da hukumar ke zargin shi da watsi da gayyatar da ta yi mishi domin bincike akan shi.

Wata majiyar ta ce: "Hukumar ta bada tabbacin cewa zata bi umarnin kotu a daga yanzu zuwa kowane lokaci, saboda mun ba shi lokaci mai yawa domin ya amsa gayyatar mu amma yaki.

"Maimakon ya bayyana a gaban hukumar mu, sai ya fara kawo mana uzuri, sannan ya rubuta mana takarda cewar zamu iya samun shi ne a cikin watan Disamba a wannan shekarar. Saboda haka daga yanzu zuwa kowanne lokaci zamu dirar masa.

"Mun gudanar da bincike na farko amma duk da haka muna bukatar Ogor ya bayyana don amsa wasu tambayoyi. Ma'aikatan mu sun gano mafi yawan ayyukan da Mista Ogor ya bayar, ya bayar dasu ne ga wasu kamfanoni guda shida, wanda duka yake da dangantaka da su.

"Kamfanonin sune: Laurelton Global Services Limited; Zanny Concern Limited; Racen Integrated Global Nigeria Limited; Simplified Concept Limited; Fergio Ventures Nigeria Limited da kuma Peanard Nigeria Limited.

"Sannan an sama kudade kamar haka a cikin asusun wadannan kamfanoni: Laurelton Global Services Limited (N101,149,293.96); Racen Integrated Global Nigeria Limited (N5,088,293.50); Peanard (N2,370,901.44); Zanny Concern Limited (N8,374,173.28) sai kuma Simplified Concept Limited (N7,000)."

Ayyukan kwamtin 'yan gudun hijira sun hada da samar da motoci manya guda uku; da motoci kirar Toyota guda uku masu daukar mutum 18; babur mai kafa uku guda 68; janareto guda 220; sai kuma babur guda 220 da dai sauran su.

Ayyukan hukumar ilimi (UBEC) da kuma sauran kamfanoni sune: Zanny (19/11/2014) - ginin ajujuwa guda uku a makarantar firamare na Eru, akan kudi N9,180,835.45; Laurelton (19/11/2014) ginin ajujuwa guda uku a makarantar firamare na Ivori, akan kudi N9,887,778; Racen (19/11/2014) gina dakunan ajujuwa guda uku a makarantar firamare ta Egburie, Ozoro; da kuma ginin ajujuwa guda shida da aka bayar a ranar 21 ga watan Janairun 2016 a makarantar firamare ta, Ozoro akan kudi N9,300,000.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel