Nigerian news All categories All tags
Buhari ne keda kasa, yana iya ziyara a ko wani lokaci - Ortom

Buhari ne keda kasa, yana iya ziyara a ko wani lokaci - Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne uban kasa sannan kuma yana iya ziyartan ko wani jiha a duk lokacin da ya yi ra’ayi.

Gwamna Ortom wanda yayi magana ta baki sakataren labaransa, Terver Akase ya bayyana cewa Benue na daga cikin yankin Najeriya sannan kuma yana iya ziyartan su.

Da aka tambaye shi ko gwamnati na farin ciki da ziyarar da kuma zaton su, Terver yace, “babu wani abu da zan fada sama da haka.

Buhari ne keda kasa, yana iya ziyara a ko wani lokaci - Ortom

Buhari ne keda kasa, yana iya ziyara a ko wani lokaci - Ortom

“Shugaban kasar keda kasa sannan kuma yana iya ziyartan ko ina a duk lokacin da ya so.”

KU KARANTA KUMA: Babu wani haraji da muka karawa masu ibada - Saudiyya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata ci gaba da karfafa alaka tare da hukumomin gargajiya a kasar domin samar da mafita mai dorewa ga rikicin makiyaya da manoma.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu a Jalingo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel