Gwamnatin jihar Sokoto ta waye Naira 7.9 miliyan don masu ciwon 'hauka' da sauran su

Gwamnatin jihar Sokoto ta waye Naira 7.9 miliyan don masu ciwon 'hauka' da sauran su

Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta amince da fitar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 7.9 domin biyan kudin magunguna da kuma na asibiti ga masu karamin karfi dake zaune a jihar.

Shugaban hukumar Zakka da wakafi na jihar ne dai Malam Lawal Maidoki ya sanar da hakan ga manema labarai lokacin da yake rarraba kudaden ga wasu asibitoci da dakunan shan maganin da jihar ta ware domin shirin.

Gwamnatin jihar Sokoto ta waye Naira 7.9 miliyan don masu ciwon 'hauka' da sauran su

Gwamnatin jihar Sokoto ta waye Naira 7.9 miliyan don masu ciwon 'hauka' da sauran su

KU KARANTA: Kwankwaso yayi fatali da batun sulhun sa da Ganduje

Legit.ng dai ta samu cewa asibitocin da suka samu shiga shirin sun hada da asibitin koyarwa ta Usmanu Danfodiyo, asibitin mahaukata dake Kware, asibitin kashi dake Wammako kuma asibitin mata da kananan yara ta Maryam Abacha duk dai a jihar.

A wani labarin kuma, Hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Economic and Financial Crimes Commission EFCC, a takaice ta kama ma'aikatan duk da suke zargi da satar kudin hukumar jarabawar share fagen shiga Jami'a watau Joint Admissions and Matriculation Board, JAMB.

Cikin wadanda aka kama hadda matar nan da zancen ta ya shahara dake aiki a ofishin JAMB din na jihar Benue dake garin Makurdi mai suna Philomina Chieshe wadda ta ce maciji ne ya hadiye kudaden hukumar har Naira miliyan 36.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel