Ya rasa ransa a rububin kwasar kudin da dan majalisa ya watsa

Ya rasa ransa a rububin kwasar kudin da dan majalisa ya watsa

- Wani yaro mai shekaru 13 ya gamu da ajalinsa yayin da yake kokarin tsintar kudin da dan majalisar yankin su ya watsa a kan titi

- Rahotanni sun bayyana cewar wata mota ce ta make yaron maj suna Bappah Adamu yayin da yake kokarin tsinto kudin

- Dan majalisar, Halliru Jika, ya watsa kudin ne lokacin da ya kai ziyarar aiki a kauyen su yaron mai suna Konkiyel a jihar Bauchi

Halin kunci ta talauci kan jefe 'yan Najeriya cikin hadari a lokuta da dama. Sau da yawa zaku ji cewar wani ko wata ya rasa ransa yayin kokarin samun abinda bai kai ya kawo ba.

Wani yaro ne dan kimanin shekaru 13 mai Suna Bappa Adamu ya rasa ransa sa sakamakon rububin dibar kudin da wani dan majalisa ya watsa a dai-dai kan hanyar Bauci zuwa Maiduguri.

Ya rasa ransa a rububin kwasar kudin da dan majalisa ya watsa

majalisar wakilai

Rahotanni sun bayyana cewa yaron ya rasu ne sakamakon mota da ta banke shi lokacin da ya ke kokarin shiga cikin masu rububin diban kudin da dan majalisar wakilai, Halliru Jika, mai wakiltar yankin Ganjuwa/Darazo ya watsa.

DUBA WANNAN: Ma’aikatan tsaron jami’ar ABU sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane su biyu

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Konkiyel lokacin da dan majalisar ya kai wata ziyarar duba aiki a yankin.

Wannan abin takaici na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka fara buga gangar siyasa kuma 'yan siyasa su ka fara neman goyon bayan masu zabe.

Majiyar mu bata samu jin ta bakin iyayen yaron ko dan majalisar da ya watsa kudin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel