Nigerian news All categories All tags
Mu na da buri sosai akan zaben 2019 na Najeriya - Kasar Amurka

Mu na da buri sosai akan zaben 2019 na Najeriya - Kasar Amurka

Kasar tarayyar Amurka ta bayyana cewa ko shakka babu idanun ta yana kan kasar Najeriya musamman ma wajen yadda za ta gudanar da zabukan ta na shekarar 2019 mai zuwa cikin ingantaccen yanati da tsafta duba da muhimmancin kasar ga zaman lafiyar nahiyar ta Afrika.

Wannan dai ya fito bakin Sakataren harkokin wajen kasar ne Mista Rex Tillerson yayin ziyarar da ya kawo ta aiki zuwa nahiyar ta Afrika kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai.

Mu na da buri sosai akan zaben 2019 na Najeriya - Kasar Amurka

Mu na da buri sosai akan zaben 2019 na Najeriya - Kasar Amurka

KU KARANTA: Kano ba sulhu: Kwankwaso yayi fatali da gayyatar kwamitin sasanci

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Sakataren na harkokin wajen kasar har ila yau zai kuma gana da shugaba Muhammadu Buhari da sauran wasu manyan shugabannin kasashen na nahiyar yayin ziyasar ta sa daga 6 zuwa 13 ga watan Maris.

A wani labarin kuma, Wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi wani taron sirri a daren ranar Lahadi a can garin Gombe bayan kamma taron majalisar zartarwar jam'iyyar da ya gudana a gidan gwamnatin jihar ta Gombe.

Kamar dai yadda muka samu da majiyoyin mu kuma, gwamnonin sun tattauna ne a kan yadda za su fito da gwamnan jihar ta Gombe da yanzu haka yake kare wa'adin mulkin sa a shekarar 2019 domin ya gwabza da shugaba Buhari.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel