Nigerian news All categories All tags
Ana zargin gidan marayun jihar Kaduna suna sayar da marayun da aka damka musu amana

Ana zargin gidan marayun jihar Kaduna suna sayar da marayun da aka damka musu amana

- Gwamnatin Kaduna ta bayyana damuawarta akan zargin da ake yiwa gidan marayun jihar Kaduna na fataucin kanana yara

- Kwamsihinan ma’aikatar hakar mata da walwala ta jihar Kaduna ta kai karar gidan marayun jihar Kaduna zuwa ga hukumar NAPTIP

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana damuwar ta akan zargin da ake yiwa gidan marayayun Kaduna na cewa suna sayar da marayun da aka damka musu amana ga mutanen kasashen waje

An dai yi zargin ne sakamakon wani hukuncin da Babbar Kotun Kaduna ta bayar cewa a damka wasu yara uku ga wani dan kasar Ghana da gwamnati ta yi zargin cewa sayen yaran ya yi da tsabar kudi har naira milyan N1.1m.

‎Kwamishinan hakar mata da walwala ta jihar Kaduna,Hajia Hafsat Baba, ta bayyana haka ne a zanatwar da ta yi da manema labaru a ranar Asabar.

Ana zargin gidan marayun jihar Kaduna suna sayar da marayun da aka damka musu amana

Ana zargin gidan marayun jihar Kaduna suna sayar da marayun da aka damka musu amana

Hajia Hafsat Baba, ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta na fargabar cewa ana neman a mayar da jihar wata cibiyar fataucin kananan yara.

KU KARANTA : Ba abun da zai iya hana siriki na zama gwamnan jihar Imo – Rochas Okorocha

Ta ce ma’aikatar hakar mata da walwala ta jihar Kaduna ta sanar da Hukumar hana fataucin mutane na Najeriya (NAPTIP) akan wannan al’amari

Kuma ta kara da cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa dokar hana fataucin yara, wadda nan ba da dadewa ba Gwamna Nasir El-Rufai zai rattaba hannu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel