Nigerian news All categories All tags
Zamu karfafa hukumomin gargajiya domin magance rikin makiyaya da manoma

Zamu karfafa hukumomin gargajiya domin magance rikin makiyaya da manoma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata ci gaba da karfafa alaka tare da hukumomin gargajiya a kasar domin samar da mafita mai dorewa ga rikicin makiyaya da manoma.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu a Jalingo.

Shugaba Buhari, wanda ya samu rakiyan gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, ya tattauna da kungiyar shugabannin gargajiya, shugabannin garuruwa, wakilan manoma da makiyaya da kuma jami’an gwamnatin jiha.

Shugaban kasar ya ce ana bukatar cikakken goyon bayan hukumomin gargajiya domin dawo da zaman lafiya musamman domin su zasu koya wa magoya bayansu yanda zasu daraja al’amuran rayuwa.

Zamu karfafa hukumomin gargajiya domin magance rikin makiyaya da manoma

Zamu karfafa hukumomin gargajiya domin magance rikin makiyaya da manoma

Ya fada ma sarakunan cewa gwamnati ta jajirce wajen ganin ta magance rikicin makiyaya da manoma domin ganin zaman lafiya ya wanzu.

KU KARANTA KUMA: Kai dan ta'adda ne jahili makiyin jihar Kaduna – El-Rufai ga Shehu Sani

Shugaban kasar ya yi gargadin cewa za a binciki dukannin wadanda suka haddasa rikici kasar sannan kuma za a hukunta su. Sannan yayi ta’aziya ga iyalan wanda abun ya shafa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel