Assha: An kama wani mahaifi da dansa da ke sayar wa dalibai frimare miyagun kwayoyi

Assha: An kama wani mahaifi da dansa da ke sayar wa dalibai frimare miyagun kwayoyi

- Jami'an Yan Sanda sun kama wani mutum tare da dan sa da ke sayar wa daliban frimari da sakandare muggan kwayoyi

- Hukumar Ilimi na jihar Legas ne ta tsegunta wa yan Sanda batun bayan sa ido kan yadda dabi'un wasu daliban makarantar ya sauya

- Shehu Ibrahim mai shekaru 45 da amsa cewa ya na sayar da kwayoyin Tramadol da wasu kwayoyin da ke saka maye amma ya ce manya kawai ya ke sayar wa

Wani dan shekara 45 mai suna Shehu Ibrahim, tare da dan sa mai suna Farooq mai shekaru 22, sun shiga hannun hukuma bisa ga laifin sayar da kwayar Tramadol da Tramol ga yara ‘yan makarantun frimare da Sakandare a unguwar Itire na jihar Legas.

Assha: An kama wani Mahaifi da dansa da ke siyar wa dalibai miyagun kwayoyi
Assha: An kama wani Mahaifi da dansa da ke siyar wa dalibai miyagun kwayoyi

Hukumar yan Sanda ta 'Rapid Response Squad' na jihar Legas suka yi awon gaba da su a ranar Juma’a, bayan da wasu ma’aikatan hukumar Ilimi ta kai ko ke akan yanda yara ke shan kwayoyi a makarantu. Inda bayan bincike da sa ido akan al’amuran yara aka yi nasarar kama masu saida masu, wanda aka same su da kwayoyin na Tramadol da Tramol har ma da wasu kalar kwayoyin

KU KARANTA: 'Dan kunar bakin wake ya kashe jami'an tsaro 3, ya kuma raunana mutum 17 a Borno

Ibrahim yayi musu akan maganar sayar wa yaran kwayoyi, shima dan nasa ya nuna bashi da masaniya a kan hakar inda ya ke cewa baban nasa yana sayarwa manya ne kawai da kwayar. Amma wani karamin yaro ya taba zuwa siya saidai shi bai sayar ma sa ba amma bai sani ba ko mahaifin nasa ya sayar masa daga baya.

Kwamishinan na ‘Yan Sanda, Edgal Imohimi, ya shawarci iyaye da ma’aikatan da su zama masu sa ido kan yaransu. Bayan nasarar da ya samu ta kara kama wasu ‘yan fashi da makami wanda suka kware a bangaren satar motoci, suna daukar motocin daga

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164