Nigerian news All categories All tags
Mutane kusan 100 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa a Najeriya

Mutane kusan 100 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa a Najeriya

- Mutane fiye da 90 ne cutar Lassa ta kashe kwanan nan a cikin Najeriya

- Ministan lafiya yana ganin akwai sakacin Jihohi wajen barkewar cutar

- Ana kira ga Jama’a su zama masu tsabta domin gudun kamuwa da cutar

Mun samu tabbacin cewa akalla mutum 90 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa da ta kara dawowa Najeriya da wasu Yankin Afrika. Kawo yanzu dai Hukumar da ke kula da cututtuka tace sama da mutane 1000 sun kamu da cutar.

Mutane kusan 100 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa a Najeriya

Annobar da ta dawo Najeriya na cigaba da kashe jama'a

Hukumar ta NCDC ta kasar ta bayyana cewa zazzabin cutar Lassa tayi sanadiyyar rasa dinbin jama’a a cikin Jihohin Najeriya 18. Yanzu haka cutar ta shiga Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Anambra, Benuwe, Kogi, Imo, Filato, Legas, da ma Jihar Taraba.

KU KARANTA: Wani Likita ya karya hannun jariri wajen karbar haihuwa

Kamar yadda mu ka samu labari har a Jihar Delta, da Osun, Ribas, Gombe, Ekiti.da Birnin Tarayya ana fama da wannan annoba. Malaman asibiti kusan 14 su ka rasu a Johohin kasar. Ministan lafiya Isaac Adewole dai ya zargi Kwamishinonin lafiya da sakaci.

Yanzu Hukumar NCDC ta zuba Jami’ai a Iyakokin kasar domin hana cutar zagayawa. Kashi 21% na wanda su ka kamu da cutar dai su na rasuwa ne kamar yadda bincike ya nuna. Malaman lafiya su na kira a zauna cikin tsabta domin gudun kamuwa da cutar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel