Nigerian news All categories All tags
EFCC ta sake gano wasu ma'aikatan JAMB da suka kware wajen karkatar da kudade

EFCC ta sake gano wasu ma'aikatan JAMB da suka kware wajen karkatar da kudade

Hukumar kiyaye cin hanci da rashawa wato EFCC ta bankado wasu gungun ma'aikatan JAMB wanda suka kware wajen karkatar da kudin hukumar zuwa asusun ajiyar su kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumar ta EFCC tana cigaba da bincikar ma’aikaciyar na JAMB daga Jihar Makurdi, Philomina Chieshe, wanda tayi ikirarin cewa maciji ya hadiye N36m na wasu daga cikin kudin da aka samu wurin saida katin JAMB wanda aka fi sani da scratch card.

Badakalar N36m a JAMB: EFCC ta cafke wasu ma'aikata da ake zargi da hannu cikin bacewar kudin

Badakalar N36m a JAMB: EFCC ta cafke wasu ma'aikata da ake zargi da hannu cikin bacewar kudin

Chiese ta bayyana wa hukumar ta EFCC cewa ta karbi kudaden ne daga hannun ubangidan ta mai kula da ayyuka, Mr. Samuel Umoru, ma’aikacyar ta JAMB a jihar makurdi ta kuma kara da cewa shine yake sanya ta fitar da kudaden na cinikin katin daga bankunan da suke ajiye.

KU KARANTA: 'Dan kunar bakin wake ya kashe jami'an tsaro 3, ya kuma raunana mutum 17 a Borno

Majiya Legit.ng nuna an dade ana aikata irin wannan barna kafin a kafa asusun ajiya na bai daya wanda ake kira Single Treasury Account, wanda a lokacin kafin wannan tsari ma’aikatar ta JAMB suna ajiyar kudin katin a asusun ajiya na su, wanda sakamakon hakan biliyoyin kudade ne suka salwanta ta wannan hanyar. Tuni dai an tabbabtar da cewa Hukumar ta EFCC ta kama Umoru, bisa ga bayanan da ta ji daga chieshe, duk da cewa an bada shi beli.

Hukumar dai ta kuma kara damke wani ma’akacin a jihar Gombe wanda aka samu da laifin kasa yin bayani na inda N20m ta shige na kudin kati, duk da dai ya musunta aikata hakan a lokacin da yake bayani a ofifshin hukumar ya nuna cewa sa hannun ma da aka gani a takardar karbar katin bashi ya yi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel