Nigerian news All categories All tags
Ziyarar Buhari Ihu Ne Bayan Hari – PDP

Ziyarar Buhari Ihu Ne Bayan Hari – PDP

- Jam'iyyar PDP ta soki shugaba Buhari akan shirin ziyaratar jihohin dake fusakanta mastalar tsaro a Najeriya

- PDP ta ce shirin ziyarar Buhari ihu ne bayan hari

Babban jam’iyyar adawa ta PDP ta ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya makara a ziyarar da zai fara zuwa jihohi dake fuskantar matsalolin tsaro a fadin kasar, musamman jihar Yobe da aka sace ‘yan mata 110 a GSS Dapchi.

Jam’iyar People’s Democratic Party PDP ta ce ziyarar Buhari a yanzu ihu bayan hari.

Ziyarar Buhari Ihu Ne Bayan Hari – PDP

Ziyarar Buhari Ihu Ne Bayan Hari – PDP

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita, PDP ta ce abin damuwa ne a ce sai bayan watannin shugaba zai ziyarci wurare da mahara daban-daban suka ci karansu babu babbaka a cikin kasar sa.

KU KARANTA : 'Yan majalisar Najeriya sun shirya yin fito na fito da Buhari akan kin amincewa da kafa rundunar 'Peace Corps'

A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Litinin, Ta ce shugaba Buhari zai ziyarci jihar Yobe, Zamfara, Taraba, Ribas da Benuwe.

A lokacin da manema labarai suka tambayi gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ko yana maraba da shirin ziyarar jihar sa da shugaba, Buhari, zai yi a yanzu, Gwmnan ya ce shugaban kasa, shine mai kasa kuma yana da ikon ziyartar ko’ina a kasar a lokacin da yaga dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel