Nigerian news All categories All tags
Yan sanda sun kama mahaukaci da bindiga a Lagas (hoto)

Yan sanda sun kama mahaukaci da bindiga a Lagas (hoto)

- An kama wani mahaukacin karya mai shekaru 35 a jihar Lagas

- An kama shi ne da bindigar wasan yara a karkashin gadar Eko Bridge

- Ya tona asirin cewa yana amfani da bindigar ne wajen tsorata masu gibtawa sannan yayi masu fashin kayayyakin su

Jami’an yan sandan RSS sun kama wani mahaukacin karya a karkashin gadar Eko bridge dake jihar Lagas.

Mutumin wanda ya bayyana kansa a matsayin Oyahere Johnson, mai shekaru 35 daga Port Harcourt ya tona asirin cewa yana amfani da bindigar wasan ne wajen yiwa mutane fashi.

Yan sanda sun kaama mahaukaci da bindiga a Lagas

Yan sanda sun kaama mahaukaci da bindiga a Lagas

Ya bayyana cewa yana amfani dab akin bindigan wasa wanda yayi kama da bindigar Baretta wajen yiwa masu wucewa fashin kudade da sauran kayayyaki.

KU KARANTA KUMA: Dattawan Kwankwaso sunyi Allah wadai da furucin Rabiu Kwankwaso kan auren yar Ganduje

Jami’an yan sanda RRS ne suka kama shi bayan wani dan achaba ya kai masu rahoto da misalign karfe 11 na dare a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris.

Jami’an sun je wajen da abun ke afkuwa cikin gaggawa sannan kuma suka gano mutumin inda ya boye bindigar a wandonsa sannan yayi yunkurin guduwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel