Nigerian news All categories All tags
2019: Wani babban 'Dan APC ya roki Shugaba Buhari ya karasa ladan sa

2019: Wani babban 'Dan APC ya roki Shugaba Buhari ya karasa ladan sa

- Anyim Nyerere ya roki Shugaban Kasa Buhari ya nemi zarcewa a zaben 2019

- Babban 'Dan siyasar yace akwai bukatar Shugaba Buhari ya karasa aikin sa

- Tsohon 'Dan takarar Gwamnan ya kuma ya yabawa kokarin Jam'iyyar APC

Mun samu labari cewa wani Jigo a Kudancin Najeriya na Jam'iyyar APC Nyerere Anyim ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2019.

2019: Wani babban 'Dan APC ya roki Shugaba Buhari ya karasa ladan sa

An roki Shugaba Buhari ya fito takara a 2019

Nyerere Anyim wanda shi ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Abia a zaben 2015 yayi kira ga Shugaban kasa Buhari ya zarce kurum domin karasa ladan sa lokacin da yayi hira da gidan Jaridar Daily Post a gidan sa.

KU KARANTA: Shugaban Jam’iyyar APC UK ya nemi Buhari ya cika alkawuran 2015

Babban 'Dan APC ya roki Shugaban kasar ya ji kukan mafi yawan 'Yan Najeriya da ke neman sa ya kara fitowa zabe. Nyerere yace duk Najeriya babu 'Dan siyasar da zai iya doke Shugaban kasa Buhari a zabe a Najeriya.

Wannan Babban 'Dan siyasar kasar nan wanda yana cikin manya a Gwamnatin Buhari ya ce Shugaban kasar na bakin kokari kuma Jam'iyyar APC tayi daidai na kara wa'adin Shugaban ta John Oyegun yace yanzu 2019 ake hari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel