Nigerian news All categories All tags
Muna kara baza komar mu a fadin Najeriya domin dakile aiyukan ta'addanci - Buratai

Muna kara baza komar mu a fadin Najeriya domin dakile aiyukan ta'addanci - Buratai

- Shugaban dakarun sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce hukumar soji na kara yawan sansanin soji domin dakile aiyukan ta'addanci

- Buratai ya bayyana haka ne yayin kaddamar da wata barikin soji a Yenagowa, babban birnin jihar Bayelsa

- Ya bayyana cewar hakan ya zama dole domin cinma manufar gwamnatin shugaba Buhari ta yaki da aiyukan ta'addanci

Shugaban rundunar sojin kasa ta kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewar hukumar soji na kara yawan sansanin soji a fadin Najeriya domin dakile aiyukan ta'addanci.

Shugaban sojin ya bayyana haka ne yayin bikin bude wata sabuwar barikin soji a Elebele dake Yenagowa, babban birnin jihar Bayelsa.

Muna kara baza komar mu a fadin Najeriya domin da dakile aiyukan ta'addanci - Buratai

Laftanal Janar Yusuf Buratai

Ya kara da cewar, shugaba Buhari, ba zai cinma manufar sa ta samar da tsaro ba muddin hukumar soji bata fadada aiyukan ta ba.

Ya bayyana cewar bude sansanin rundunar soji na 6 a Fatakwal da kuma ta 16 a Yenagowa na daga cikin aikin hukumar na fadada komar ta.

DUBA WANNAN: Likita ya karya hakarkarin jariri a kokarin karbar haihuwa

Buratai ya kara da cewar, ki a ranar 28 ga watan Fabrairu, saida ya ya halarci kaddamar da bude wata barikin soji a Katsina da kuma wata da aka gina a Monguno, jihar Borno, duk da ya ce za a mayar da shelkwatar ta jihar Sokoto da zarar zaman lafiya ya dawo yankin arewa maso gabas.

Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da jami'an gwamnatin sa da kuma manyan dakarun soji ne su ka hakarci taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel