Bai dace Wenger ya cigaba da horas da Arsenal ba – Gwamna Aregbesola

Bai dace Wenger ya cigaba da horas da Arsenal ba – Gwamna Aregbesola

- Ana cigaba da kira a gida da ma waje a kori Arsene Wenger daga Arsenal

- Babban Kocin ya dade yana horas da Arsenal sai dai har yanzu gara jiya

- Gwamnan Jihar Osun yana cikin masu kira Kocin ya tashi ya bar Arsenal

Mun samu labari na musamman cewa Gwamnan Jihar Osun watau Rauf Ogbeni Aregbesola yana cikin masu kira Kocin kungiyar Arsenal ya tattara kayan sa ya bar Kungiyar.

Bai dace Wenger ya cigaba da horas da Arsenal ba – Gwamna Aregbesola

Gwamna Arebosola yace ya kamata Wenger ya hakura da Arsenal

Bisa dukkan alamu dai Gwamnoni ma dai na samun lokacin watayawa tun da har kuwa su na kallon wasan kwallon kafa. Shi dai musamman Gwamna Rauf Aregbesola na Jihar Osun rikakken magoyin bayan Kungiyar Arsenal ne.

KU KARANTA: Dangote na neman sayen Kungiyar Arsenal nan gaba

Sai dai kwanan aka kara dirkawa Arsenal ci a wasan ta Gasar Firimiya. Wannan abu dai ya kara harzuka Magoya bayan Kungiyar wanda su ke ta fafatukar ganin an tsige Kocin su Arsene Wenger wanda ya jima yana horaswa a Kungiyar.

Shi ma Aregbesola ba a bar sa a baya ba inda yayi amfani da shafin sa na sada zumunta na Tuwita a karshen makon nan yace zai yi wahala Wenger ya cigaba da horas da Arsenal. Gwamnan yayi wannan jawabi be bayan Brigton ta ba kungiyar kashi

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel