Nigerian news All categories All tags
Matashi ya yi yunkurin kashe mahaifiyar sa bayan kisan mahaifinsa

Matashi ya yi yunkurin kashe mahaifiyar sa bayan kisan mahaifinsa

- Wani matashi, Ifeanyi Oguejiofor, ya hallaka mahaifin sa sannan ya yi yunkurin kashe mahaifiyar sa

- Lamarin ya faru ne ranar Asabar a kauyen Abatete dake karamar hukumar Idemili ta arewa a jihar Abiya

- 'Yan kungiyar kato da gora sun yi nasarar damke shi tare da mika shi hannun hukumar 'yan sanda

Wani matashi Ifeanyi Oguejiofor ya yi yunkurin kashe mahaifiyar sa bayan ya hallaka mahaifin sa.

Rahotanni sun bayyana cewar matashin ya caccakawa mahifin nasa wuka sannan ya soki mahaifiyar sa da wukar, da niyyar kashe ta.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar a garin Abatete dake karamar hukumar Idemili ta arewa a jihar Anambra.

Matashi ya yi yunkurin kashe mahaifiyar sa bayan kisan mahaifinsa

'Yan sandan Najeriya

Wannan ibtila'i na faruwa ne cikin kasa da sati guda bayan wani mutum ya kashe matar sa da 'ya'yan su hudu a karamar hukumar.

'Yan kungiyar kato da gora sun yi nasarar damke matashin tare da mika shi hannun hukumar 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Wuta ta kone su bayan sun fasa bututu domin satar danyen man fetur

Mahaifiyar sa da ta rayu ta bayyana cewar matashin ya kashe mahaifin nasa ne saboda ya hana shi kudi, kuma ita ma a kan hakan yaso hallaka ta.

Matashin, mai sana'ar acaba, yanzu haka na hannun hukumar inda ake cigaba da bincike.

Ba a samu jin ta bakin kakakin hukumar 'yan sanda, Nkeiruka Nwode, a jihar ba bayan kiran lambobin wayar ta dake a kashe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel