Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasan Liberia, George Weah

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasan Liberia, George Weah

A yanzu haka, shugaba Muhammadu Buhari na karban bakuncin shugaban kasan Liberiya, George Weah, a fadar shugaban kasa, da ke babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Weah ya isa fadar shugaban kasa ne misalin karfe 12:34 an ranan kuma shugaba Muhammadu Buhari ya tarbesa.

Tsohon shahrarren dan kwallon kafan ya kasance sanata ne mai wakiltan mazabar Montserrado County a majalisar dattawan kasan daga 14 Janairu 2015 zuwa 22 Janairu 2018.

Weah ya shiga harkar siyasa ne bayan ritaya daga kwallon kafa. A shekarar 2005, ya yi takaran shugaban kasa amma ya sha kasa.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasan Liberia, George Weah

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasan Liberia, George Weah

Kana a shekarar 2011, ya sake takara a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da Winston Tubman amma ya sake shan kasa.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun koka akan yadda aka cigaba da sa su yin aikin ‘yasanda

Amma bai gaji ba, sai ya sake takara a shekarar 2017 inda ta kada mataimakin shugaban kasa. Boakai kuma aka rantsar da shi ranan 22 ga watan Janairul 2018.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel