Nigerian news All categories All tags
Zuciya ƙwan fitila: Wani dan majalisa ya wancakalar da kujerarsa don nuna ɓacin rai game da hamɓarar da gwamnatin Mugabe

Zuciya ƙwan fitila: Wani dan majalisa ya wancakalar da kujerarsa don nuna ɓacin rai game da hamɓarar da gwamnatin Mugabe

Wani dan majalisa a kasar Zimbabwe ya yi murabus daga mukaminsa na dan majalisa don nuna bacin ransa game da hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe.

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito dan majalisar mai suna Ambrose Muntinhiri da ya fito daga jam’iyya mai mulkin kasar, ZANU-PF ya aika ma Kaakakin majalisar dokokin kasar Zimbabwe, Jocob Mudenda da wasikar sa ta murabus.

KU KARANTA: ‘Adan ina son ka, don Allah ka ajiye wukar ‘ – Inji wata bazawara a lokacin da tsohon Mijinta ya caccaka mata wuka

A cikin wasikar, Mutinhiri wanda na hannun daman Mugabe da magtarsa Grace ne, ya shaida ma Kaakakin matsayin da ya dauka na ficewa daga jam’iyyar, tare da yin murabus daga kujerarsa ta dan majalisa,kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Zuciya ƙwan fitila: Wani dan majalisa ya wancakalar da kujerarsa don nuna ɓacin rai game da hamɓarar da gwamnatin Mugabe

Mugabe da Mutunhiri

“Tuni na yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar ZANU-PF tare da wancakalar da mukami na, duba da yadda aka yi ma doka karan tsaye wajen kawar da gwamnatin tsohon shugaba kasa Robert Mugabe tare da maye gurbinsa da Emmerson Mnangagwa a watan Nuwambar 2017.” Inji shi.

Shi dai Muntihiri, baya ga kasancewa dan majalisa, shi ne kuma kula da al’amuran lardin gabashin Masholand na kasar Zimbabwe, sai dai sabon shugaban kasar ya hana mukamin, inda rahotanni ke ganin zai jagoranci kafa jam’iyyar da Mugabe da matarsa zasu shiga, mai suna New Patriotic Front(NPF).

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel