Nigerian news All categories All tags
Idan ba tsoro ba: Duk abinda ya El-Rufai ke ji, ya tara ya samu – Inji Sanata Shehu Sani

Idan ba tsoro ba: Duk abinda ya El-Rufai ke ji, ya tara ya samu – Inji Sanata Shehu Sani

Sanata mai wakiltar jama’an Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa duk abinda da gwamna El-Rufai ke ji da shi, ya tara ya samu, “Idan yaki yak enema, mun shirya ma babban yaki.”

The Cables ta ruwaito Sanatan ya bayyana haka ne bayan ganawa da kwamitin jin bahasi wanda uwar jam’iyyar APC ta aiko ta jihar Kaduna don jin bayanai daga dukkanin bangarorin jam’iyyar a jihar da basa hga maciji.

KU KARANTA: Don bukatar kashin kai wasu Kwamishinoni na amfani da tsafe tafe wajen juya gwamnansu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shehu Sani da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ba sa zama a inuwa guda, wanda ya janyo tsagin APC da ke biyayya ga su Shehu Sani ya dakatar da gwamnan daga jam’iyyar, inda shi kuma gwamnan ya rusa ofishin da suke ikirarinsa a matsayin ofishin jam’iyya.

Idan ba tsoro ba: Duk abinda ya El-Rufai ke ji, ya tara ya samu – Inji Sanata Shehu Sani

Sanata Shehu Sani

“Idan wani na da niyyar ayi sulhu, wani kuma bashi da wannan niyya, babu inda zamu je, don haka ina goyon bayan duk wani sulhu da za’yi. Matsayin mu shi ne, idan gwamnan jihar Kaduna na son zaman lafiya, za’a zauna lafiya, idan kuma yaki ya nema, mun shirya ma babban yaki.” Inji Sani.

Sai dai Sanata ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga tsakani a rikicin siyasar da ta dumama jihar Kaduna, inda yace Buhari Uba ne ga kowa, don da ba don Buhari ba, da kowa ya kama gabansa, don haka ya zama wajibi ya magance rikita rikitan nan.

“Mun mika bayananmu ga kwamitin Segun Oni, wanda muke sa ran zasu mika shi ga kwamtin sulhu wanda Tinubu yake jagoranta, kuma muna sa ran zasu yi mana adalci.” Inji shi

Sai dai daga karshe, Sanatan yace “idan kuma wani mutumi na ganin shi kadai ke da jam’iyyarnan, kuma yana ganin bani da wani amfani a cikinta, sai in fice na bashi wuri.” tun da dai ba zaman wani yake ba a cewarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel