Nigerian news All categories All tags
Kenya: Mara lafiyan da likita yayi kuskuren yiwa aikin tiyata ya mutu

Kenya: Mara lafiyan da likita yayi kuskuren yiwa aikin tiyata ya mutu

- Mara lafiya a asibitin kasar Kenya da likita yayiwa tiyata sabanin ainihin mai bukata ya cika

- An kai mara lafiyan asibiti ne bayan ya ya samu hadarin babur da ya shafi kwakwalwarsa

- Danginsa sunyi ikirarin cewa anyi tiyata a kan wani daban, likitoci sunce babu abinda zasu iya yanzu

Iyalan mara lafiyan da tasautsayi ya kama a babban asibitin kasar Kenya wato Kenyatta National Hospital (KNH) suna kokawa bayan dansu ya mutu sanadiyar aikin tiyatan kuskuren da akayi masa.

Mara lafiyan mai suna Angelos Miano, mai shekaru 25 da haihuwa ya mutu ranan Asabar, 3 ga watan Maris ne bayan likitoci sun ki kula da shi.

Game da cewar tashar KTN News, An kwantar da Angelo ne a asibitin bayan ya samu hadarin babur kuma ya samu rauni a kwakwalwa. Iyalan bayan biyan kudin aiki ranan 28 ga watan Fabrairu cewa ashe ba’a yi wa ainihin mai raunin aikin tiyata ba.

Kenya: Mara lafiyan da likita yayi kuskuren yiwa aikin tiyata ya mutu

Kenya: Mara lafiyan da likita yayi kuskuren yiwa aikin tiyata ya mutu

Tuni asibitn ta sallami likita da wasu ma’aikatan asibitin 3 wadanda suka aiwatar da wannan aikin kuren.

KU KARANTA: Kotun koli ta kawo karshen shari'ar Sambo Dasuki da kuma hukumar EFCC

Bai kare a nan ba, har shugaba asibitin ta samu dakatarwa sanadiyar wannan babban kuskure da ya faru karkashinta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel