Kotun koli ta kawo karshen shari'ar Sambo Dasuki da kuma hukumar EFCC

Kotun koli ta kawo karshen shari'ar Sambo Dasuki da kuma hukumar EFCC

Kotun koli ta kasa wadda ake yi wa lakabi da kotun Allah-ya-isa ta yanke hukuncin karshe a game da takaddamar shari'ar da ake ta tafkawa a tsakanin tsohon mai ba sohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fannin tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya) da ake cigaba da yi a wani boyayyen wuri na musamman.

Da suke yanke hukuncin, kotun a ta bakin babban alkalin kotun Mai shari'a Ajembi Eko ya bayyana cewa kotun ta kuma gano cewa ba hukumar EFCC ce ba ke dauke da alhakin cigaba da tsare Kanal Dasuki din.

Kotun koli ta kawo karshen shari'ar Sambo Dasuki da kuma hukumar EFCC

Kotun koli ta kawo karshen shari'ar Sambo Dasuki da kuma hukumar EFCC

KU KARANTA: Dahiru Bauchi ya gargadi masu son yi wa darika shishshigi

Legit.ng ta samu cewa kotun ta bayyana a binciken da ta yi cewar hukumar 'yan sandan farin kaya ta DSS ce ke cigaba da tsare shi bisa zargin da ake yi masa na badakalar kudaden makamai da suka kai Dalar amurka biliyan biyu.

A wani labarin kuma, Wani jigo kuma babba a jam'iyyar APC mai mulki mai suna Cif Anike Nwoga a cikin satin da ya gabata ya maka majalisar tarayyar Najeriya kotun tarayya dake zaman ta a garin Enugu inda yake kalubalantar ta da yunkurin sauya tsarin zabe a shekarar 2019.

Cif Nwoga wanda ke zaman mataimakin shiyyar kudu maso gabashin kasar na jam'iyyar ta APC ya bayyana cewa matakin da 'yan majalisar ke neman zartarwa ko kusa bai dace ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel