Nigerian news All categories All tags
Satar 'yan matan Dapchi: Abun da 'yan Boko Haram ke son cimmawa - JNI

Satar 'yan matan Dapchi: Abun da 'yan Boko Haram ke son cimmawa - JNI

Kungiyar nan ta addinin Islama ta Jama’atu Nasril Islam karkashin jagorancin Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar a karshen satin da ya gabata sun yi kakkausar suka ga gwamnatin tarayya da kuma jami'an tsaro game da satar 'yan matan makarantar Dapchi 110.

Kungiyar ta addinin islama dai ta bayyana cewa wannan sakacin na gwamnati abun takaici ne kuma ya kawo koma baya ga ilimin 'ya'ya mata a yankin na Arewacin Najeriya wanda kuma hakan ba karamin nakasu bane ga yankin.

Satar 'yan matan Dapchi: Abun da 'yan Boko Haram ke son cimmawa - JNI

Satar 'yan matan Dapchi: Abun da 'yan Boko Haram ke son cimmawa - JNI

KU KARANTA: Yan kwastam sun kama buhunnan shinkafa 460 masu guba a Sokoto

Legit.ng dai ta samu cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban Sakataren kungiyar Dakta Abubakar Khalid Aliyu ya sanya wa hannu ya kuma rabawa manema labarai a garin Kaduna inda ya bayyana cewa kamata yayi ace kawo yanzu gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki ga wadan da suka yi sakacin.

A wani labarin kuma, Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya sanar da matsayar da dukkan sarakunan gargajiyar kasar nan musamman ma na arewaci kuma musulmai suka cimmawa ta daukar nauyin marayun da rikicin Boko Haram ya kashewa yara a arewa maso gabashin kasar nan.

Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da littafin mususulci na “Fath Rabbil Bariyya,” sharhin littafin Iziyya wanda shahararren malamin addinin Islama din nan watau Dakta Mansur Sokoto ya wallafa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel