Nigerian news All categories All tags
Hukumar Kwastam ta kama buhuhunan shinkafa a cikin tankar man fetur (hoto)

Hukumar Kwastam ta kama buhuhunan shinkafa a cikin tankar man fetur (hoto)

Hukumar kwastam tace ta kama wani mai laifi a jihar Sokoto bisa zargin shigo da buhuhunan shinkafa yar waje guda 460 cikin tankar man fetur.

Kwamturollan hukumomin jihar Sokoto, Kebbi da Zamfara, Mista Nasir Ahmad, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a a jihar Sokoto.

Ahmad ya ce abubuwan fasa kwabrin da aka kama a hanyar Sokoto-Illela ya kai kimanin naira biliyan 7.8.

Ya bayyana cewa a lokacin da aka cire buhuhunan shinkafan daga tankin sun rigada sun baci da bakin mai, wanda hakan yana da matukar hatsari ga lafiyar dan Adam.

Hukumar Kwastam ta kama buhuhunan shinkafa a cikin tankar man fetur

Hukumar Kwastam ta kama buhuhunan shinkafa a cikin tankar man fetur

Ya shawarci masu fasa kwabri da su nemi mafita wajen tafiyar da rayuwarsu ta hanyar halal sannan su daina gurbata tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam

Ya roki jama’a da su dunga basu bayanai da ya dace domin taimakawa masu fasa kwabri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel