Nigerian news All categories All tags
Sarkin musulmi ya bayyana shawarar sarakunan gargajiya akan marayun Boko Haram

Sarkin musulmi ya bayyana shawarar sarakunan gargajiya akan marayun Boko Haram

Sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya sanar da matsayar da dukkan sarakunan gargajiyar kasar nan musamman ma na arewaci kuma musulmai suka cimmawa ta daukar nauyin marayun da rikicin Boko Haram ya kashewa yara a arewa maso gabashin kasar nan.

Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wurin kaddamar da littafin mususulci na “Fath Rabbil Bariyya,” sharhin littafin Iziyya wanda shahararren malamin addinin Islama din nan watau Dakta Mansur Sokoto ya wallafa.

Sarkin musulmi ya bayyana shawarar sarakunan gargajiya akan marayun Boko Haram

Sarkin musulmi ya bayyana shawarar sarakunan gargajiya akan marayun Boko Haram

KU KARANTA: Kiristoci sun fi fantama a wannan gwamnatin ta Buhari - Osinbajo

Legit.ng ta samu cewa a cewar sarkin, yanzu sarakunan sun amince cewar kowa zai dauki akalla maraya 5 da zai tarbiyantar har zuwa girman sa daga cikin wadanda suke a halin yanzu a sansanin 'yan gudun hijira.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar hukumar hana fasa kwauri ta kasa watau Kwastam shiyyar jihar Sokoto ta sanar da samun nasarar cafke akalla buhunnan shinkafa 'yar kasar waje 460 makare a cikin wata katuwar tirela da ake kokarin shigowa da ita ta barauniyar hanya.

Haka ma dai mahukunta a rundunar sun bayyana cewa shinkafar tana da tsananin hadari ga dukkan wani dan kasar da ya ci ta kasantuwar gurbacewar ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel