Nigerian news All categories All tags
'Yan Najeriya sun kusa yin ta'aziyyar jam'iyyar APC - Secondus

'Yan Najeriya sun kusa yin ta'aziyyar jam'iyyar APC - Secondus

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa yanzu fa ruwa ya kusa karewa dan kada yayin da zaben 2019 ke dada karasowa domin kuwa jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC tuni ta fara kidimewa.

Wannan ikirarin dai ya fito ne a ta bakin shugaban jam'iyyar ta PDP Mista Uche Secondus yayin da yake zantawa da wakilin majiyar mu ta wayar tarho a jiya Lahadi a garin Abuja.

'Yan Najeriya sun kusa yin ta'aziyyar jam'iyyar APC - Secondus

'Yan Najeriya sun kusa yin ta'aziyyar jam'iyyar APC - Secondus

KU KARANTA: Kiristoci sun fi cin moriyar gwamnatin Buhari - Osinbajo

Legit.ng ta samu cewa Mista Secondus har ila yau ya kuma bayyana cewa kidimewar da APC din ke yi ne ma ya sanaya yanzu take neman ta bi dukkan wata hanya kazama don ganin ta sake lashe zabukan dake tafe.

A wani labarin kuma, Wani jigo kuma babba a jam'iyyar APC mai mulki mai suna Cif Anike Nwoga a cikin satin da ya gabata ya maka majalisar tarayyar Najeriya kotun tarayya dake zaman ta a garin Enugu inda yake kalubalantar ta da yunkurin sauya tsarin zabe a shekarar 2019.

Cif Nwoga wanda ke zaman mataimakin shiyyar kudu maso gabashin kasar na jam'iyyar ta APC ya bayyana cewa matakin da 'yan majalisar ke neman zartarwa ko kusa bai dace ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel