Nigerian news All categories All tags
Karya ake yi mani, ban zabi APC a 2015 ba – Ahmad Makarfi

Karya ake yi mani, ban zabi APC a 2015 ba – Ahmad Makarfi

- Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ya karyata cewa ya zabi APC a 2015

- Dokubo Asari ya zargi Ahmad Makarfi da zaben Jam’iyyar APC a baya

- Babban ‘Dan Jam’iyyar adawar yace sam babu gaskiya a maganar Asari

Mun samu labari cewa tsohon Shugaban Jam’iyyar adawa ta PDP Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya karyata cewa ya zabi Jam'iyyar APC ne a zaben da ya wuce kamar yadda wasu ke yadawa a kasar.

Karya ake yi mani, ban zabi APC a 2015 ba – Ahmad Makarfi

Ana ce-ce-ku-ce tsakanin Ahmad Makarfi da Dokubo Asari

Sanata Ahmad Makarfi ta bakin mai magana da yawun sa ya karyata kalaman tsohon ‘Dan gwagwarmayar Yankin Neja-Delta watau Dokubo Asari wanda ya bayyanawa ‘Yan Jarida kwanaki cewa Ahmad Makarfi bai zabi Jam’iyyar PDP a zaben 2015 ba.

KU KARANTA: Shugaban Jam’iyyar APC UK ya nemi Buhari ya cika alkawuran 2015

Mukhtar Sirajo wanda shi ne ke magana a madadin tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna ya bayyana cewa Ahmad Makarfi bai taba yaudarar Jam’iyyar sa ba. Sirajo yace sai da Makarfi ya daga kuri’ar sa ga Duniya bayan ya zabi Jam’iyyar PDP a zaben da ya wuce.

Mai magana a madadin Ahmad Makarfi yace mai gidan na sa ba matsoraci bane don yayi Gwamna na shekaru 8, ya kuma yi Sanata har sau 2. Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya nemi irin su Dokubo Asari su guji yada karyar da za ta ci mutuncin jama’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel