Nigerian news All categories All tags
Ya yi ikirarin Allah ne ya aiko shi saboda irin mu'ujizar da yake nunawa

Ya yi ikirarin Allah ne ya aiko shi saboda irin mu'ujizar da yake nunawa

Wani fasto, Shepherd Bushiri, dan asalin kasar Malawi dake da babbar coci a kasar Afrika ta kudu ya yi ikirarin cewar shi 'annabin' Allah saboda irin mu'ujizar da yake nunawa.

Fasto Bushiri mai shekaru 30 a duniya fitacce ne a kasashen Afrika da ma duniya bakidaya wajen yin aiyukan ban mamaki.

Ya taba warkar da masu dauke da kwayar cutar kanjamau, sannan ya taba azurta talakawa, kuma ya taba tafiya a kan iska.

Ya yi ikirarin Allah ne ya aiko shi saboda irin mu'ujizar da yake nunawa

'Manzo' Shepher Bushiri

Dubban mutane ke jiran sa na sa'o'i masu yawa duk lokacin da zai gudanar da wa'azi. Kazalika jama'a kan yi tururuwa tun daga wasu kasashen, Turai da Asiya, domin halartar wa'azin sa.

DUBA WANNAN: Ganduje ya bawa Ajimobi mamaki bayan ya nemi a biya N50,000 a matsayin sadakin auren diyar sa

Bushiri na da manyan coci a kasashen Afrika ta kudu da kuma kasar Ghana. Sai dai wasu kasashen Afrika sun haramta masa yin wa'azi a kasashen su.

Faston kan gudanar da wa'azin sa a filayen wasa saboda yawan jama'ar da kan halarci duk inda zai yi lakca. Jama'a kan fadi kasa sumammu saboda gajiyar jiran sa ya bayyana a wurin wa'azin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel