Wata ɗalibar jinya ta shiga hannun mayakan Boko Haram a jihar Borno

Wata ɗalibar jinya ta shiga hannun mayakan Boko Haram a jihar Borno

A yayin da ake jimamin sace dalibai mata su 110 daga makarantar mata na garin Dapchi a jihar Borno, sai ga shi a ranar juma’a 2 ga watan Maris, yan ta’addan sun sake yi awon gaba da wata daliba.

Legit.ng ta samu wannan labari ne daga kawar dalibar da aka sace, mai suna Hauwa Muhammad, wanda ta ce suna kiranta a kawance da suna Mimee, dukkaaninsu dalibai a kwalejin jinya da karbar haihuwa na Maiduguri.

KU KARANTA: Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari

Wannan lamari na sace sacen yan mata dalibai a yankin Arewa, inda mata basu cika zuwa makaranta ba ya zama babbar matsala ga cigaban ilimi a yankin Arewa gaba daya, wanda hakan zai kara nesanta yara ga zuwa makaranta don gudun fuskantar irin wannan zalunci.

Wata ɗalibar jinya ta shiga hannun mayakan Boko Haram a jihar Borno

Dalibar

Ko a satin data gabata, sai da wani sanata daga majalisar dattawa ya bayyana cewa biyo baya yadda gwmanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta biya Boko Haram makudan kudade da nufin sako yan matan Chibok ya kara ma yan ta’addan kwarin gwiwar satar dalibai mata, sun samu na yi.

A wani labarin kuma, babban hafsan sojan sama, Sadik Abubakar ya tattara inasa inasa zuwa jihar Yobe da zummar sanya idanu kan yadda za’a kwato yan matan Dapchi su 110 daga hannun yan ta’addan, wanda tsagin Boko Haram na Mus’ab Albarnawi ta dauki nauyin satar su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel