Nigerian news All categories All tags
Shugaban Jam’iyyar APC UK ya nemi Buhari ya cika alkawuran 2015

Shugaban Jam’iyyar APC UK ya nemi Buhari ya cika alkawuran 2015

- Jam’iyyar APC a Kasar Ingila ta ba Shugaban Kasa Buhari shawara

- APC UK tace ya kamata a cika duk alkawuran da aka yi wa ‘Jama’a

- Bangaren Jam’iyyar ta yabawa kokarin Buhari na sulhunta ‘Yan APC

Mun samu labari cewa wani bangare na Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya cika alkawarin da su ka daukarwa ‘Yan Najeriya shekaru 3 da su ka wuce.

Shugaban Jam’iyyar APC UK ya nemi Buhari ya cika alkawuran 2015

APC da kan ta ta hurowa Shugaban kasa Buhari wuta

Shugaban Bangaren Jam’iyyar da ke Kasar Birtaniya watau APC UK Dr. Phillip Idaewor ya nemi Shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa ya cika alkawuran da su ka dauka a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015.

KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa tayi karin haske kan zaben 2019

Dr. Idaewor ya ke tabbatar da cewa duk Najeriya babu Jam’iyyar da ta ke da shiri da muradun yin gyara irin APC inda ya kara da cewa Jam’iyyar ta dauki rai da daraja. Shugaban Jam’iyyar a kasar Ingila ya kuma yi kira kan hadin kai.

Phillip Idaewor ya yabawa Shugaban kasa Buhari na nada Asiwaju Bola Tinubu domin ya shawo kan barakar da ke cikin Jam’iyyar. APC UK tace dai manyan manufofin ta su ne aiki a kasa da yi wa Jama’ar Najeriya hidima tukuru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel