Nigerian news All categories All tags
Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam

Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam

- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata da karfin kare rayuka da dukiyoyi

- Wannan ra’ayin tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ne

- Suswam yayi wannan sharhi ne kan hare-haren makiyaya a fadin kasar

Tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata da karfin kare rayuka da dukiyoyi.

Suswam yayi wannan furuci ne yayinda yake Magana da wasu kungiyar manema labarai a Makurdi, jihar Benue a karshen mako.

A cewarsa, idan ba’a magance al’amarin tattalin arziki dake kyau ba shine ke kai ga matsalolin tsaro kamar wanda kasar ke fuskanta a yanzu.

Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam

Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam

Ya bayyana cewa dalilin da yasa aka zabi APC zuwa mulki na iya kasancewa saboda ana ganin cewa gwamnatin PDP ta gazawa yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: PDP ta taya Obasanjo murnar cika shekaru 81; ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki sosai a Najeriya

Ya bayyana cewa yanzu ya rage ga yan Najeriya sun yanke shawara kan imam an rage matsalolin tsaro ko kuma sun karu a karkashin wannan gwamnatin APC.

Ya yarda cewan jam’iyyarsa ta PDP ta gaza a gwamnati amma ya kara da cewa APC bata tabuka komai ba.

A halin da ake ciki, Fasto Tunde Bakare, shugaban cocin Latter Rain Assembly (LRA), ya ce ya rasa gane mai shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 22 ke yi a bikin Kano, yayinda har yanzu ba’a saki yan mata 110 na Dapchi ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel