Nigerian news All categories All tags
PDP ta taya Obasanjo murnar cika shekaru 81; ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki sosai a Najeriya

PDP ta taya Obasanjo murnar cika shekaru 81; ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki sosai a Najeriya

- Jam’iyyar PDP ta taya tsohon shugaba Obasanjo murna yayinda ya cika shekaru 81 a ranar 5 ga watan Maris

- Jam’iyyar ta ce C if Obasanjo na daya daga cikin shugabannin mafi inganci da Najeriya ta taba samu

Jam’iyyar PDP ta taya tsohon shugaba Obasanjo murna yayinda ya cika shekaru 81 a ranar Litinin, 5 ga watan Maris.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta saki ta hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan a ranar Lahadi, 4 ga watan Maris tace har yanzu tana alfahari da tsohon shugaban kasar.

Ta bayyana cewa Obasanjo ya ba da gaggfarumin gudunmawa wajen zaman lafiya da ci gaban kasashen duniya, musamman a yankin nahiyar Afrika, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

PDP ta taya Obasanjo murnar cika shekaru 81; ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki sosai a Najeriya

PDP ta taya Obasanjo murnar cika shekaru 81; ta ce yana daya daga cikin shugabannin da suka yi aiki sosai a Najeriya

Legit.ng ta tattaro cewa jam’iyyar ta bayyana Obasanjo a matsayin dan kasa mai muhimmanci, mutun mai karfin gwiwa sannan kuma shugaba mai sadaukarwa, wanda ya yi gagarumin sadaukarwa wajen ganin ci gaba, daidaito da kuma bunkasar kasar.

KU KARANTA KUMA: Na kasa gane abunda Buhari ya je yi a bikin Kano alhalin har yanzu ba’a ga yan mata 110 ba – Bakare

Jam’iyyar ta kuma yi addu’an Allah ya ba Obasanjo lafiya, hikima da karfin yayinda yake ci gaba da yiwa kasar aiki.

A halin da ake ciki, Fasto Tunde Bakare, shugaban cocin Latter Rain Assembly (LRA), ya ce ya rasa gane mai shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 22 ke yi a bikin Kano, yayinda har yanzu ba’a saki yan mata 110 na Dapchi ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel